News
ASUU Ta Sanar Da Cewa Fiye da Manyan Lakcarori 30 Sun Bar Aiki A Jami’ar SAZU
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kungiyar Malaman jami’o’i (ASUU), reshen Jihar Bauchi, ta sanar da cewa fiye da manyan Malamai 30 sun bar aiki a jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU) mallakar jihar Bauchi.
Malaman, dukkansu masu digiri na uku (PhD), sun bar aiki ne saboda rashin walwala da Kuma tabarbarewar yanayin aiki a jami’ar.
Budaddiyar Wasika Ga Gwamnatin Najeriya (An Bar Jaki Ana Dukan Taiki Akan Lafiya)
Shugaban kungiyar ASUU na shiyya, Namo Timothy, shine ya sanar da hakan yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa jami’ar tana fuskantar barazanar durkushewa saboda barin aikin kwararrun Malamai da suke da ilimi mai zurfi.
Timothy ya bayyana cewa jami’ar bata da tsarin biyan fansho ko hakkin mutuwa kamar yadda yake a tsarin hakkokin ma’aikata na kasa.
Ya kara da cewa rashin biyan fansho da sauran hakkokin ma’aikata hadi da tabarbarewar yanayin aiki ya saka Lakcarorin jin cewa basu da madafa ko majingina idan suka cigaba da aiki a jami’ar.
A cewar Timothy, duk da Karin kudin rijistar dalibai da jami’ar ke yi da Kuma kudaden shiga da take samu hakan bai sa an bawa walwalar ma’aikata fifiko ba.
A karshe ya yi kira ga gwamnatin jihar Bauchi a kan ta dauki mataki ta hanyar kawo gyara a shugabancin jami’ar da inganta yanayin aiki da walwalar ma’aikata.
WIKKI TIMES ta ruwaito cewa Lambar wayar kwamishinar ilimi ta jihar Bauchi, Jamila Dahiru, bata shiga ba yayin da aka kira ta domin Jin ta bakin ta a kan lamarin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
