News
Mummunar Gobara Ta Babbake Motar Makaranta Tare Da Hallaka Fiye Da Yara 20
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Mummunar gobarar ta babbake motar dake kan wata babbar hanya a yankin arewacin birnin Bangkok yayin da take dauke da yara 38-da suka hada da kanana da matasa da malamai 6 dake balaguron ‘yan makaranta.
Masu aikin ceto na kokarin zakulo gawawwakin yaran da suka babbake daga cikin karekitan motar safar ‘yan makaranta a kasar Thailand wacce ta kama da wuta bayan da tayi hatsarin, da ake fargabar ya hallaka fiye da mutane 20.
ASUU Ta Sanar Da Cewa Fiye da Manyan Lakcarori 30 Sun Bar Aiki A Jami’ar SAZU
Muryar Amurka ta ruwaito cewa mummunar gobarar ta babbake motar dake kan wata babbar hanya a yankin arewacin birnin Bangkok yayin da take dauke da yara 38-da suka hada da kanana da matasa da malamai 6 dake balaguron ‘yan makaranta.
Gawawwakin sun yi mummunar konewar da tasa hukumomi suka kasa tantance adadin wadanda suka mutu, sannan aikin tantance bayanan gawawwakin zai iya daukar kwanaki.
A cewar Ministan Harkokin Cikin Gidan Thailand, Anutin Charnvirakul mutane 21 sun tsira daga gobarar sai dai har yanzu ba a san inda 23 suka shiga ba amma ana kyautata zaton sun mutu.
Masu aikin ceton sun sanya shinge a kewayen tarkacen motar domin kange jami’an kashe gobara da masu bincike a yayin da suka fara aikin zakulo gawawwakin.
