News
Kaso 60 Na Al’ummar Najeriya Suna Rayuwa A Cikin Kangin Talauci —Peter Obi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar LP, a zaben shekarar 2023 Peter Obi, ya ce ayyukan ta’addanci da suka addabi kasashen nahiyar Africa sun tilastawa al’ummar yankin fadawa cikin kangin talauci.
Peter Obi ya bayyana hakan a lokacin daya halarci wani taron daya kunshi manyan shugabanni da jagororin kasashen duniya don tattaunawa akan shugabanci na gari a nahiyar Africa.
Mummunar Gobara Ta Babbake Motar Makaranta Tare Da Hallaka Fiye Da Yara 20
Inda ya zayyano cewa rashin aikin yi, cin hanci da rashawa, nuna banbanci, na daga cikin dalilan da suka hana yankin nahiyar Afrika zama cikin kwanciyar hankali da luman.
Daily News24 ta ruwaito cewa taron ya hadar da manyan jami’an gwamnati, jami’an tsaro, masana harkokin wasanni, da tsaffin sojoji, an kuma tattauna akan kalubalen da fannin tsaro ke ciki da tattalin arziki sai Kuma hasashen yanayin da za’a iya samun kai a ciki nan gab
Pater Obi, yace a matsayin su na jagororin al’umma dole ne su yi kokarin kawo wa mutane mafita daga halin kuncin rayuwa da ake fuskanta a yanzu da wanda ake hasashen samu nan gab
Tsohon gwamnan jihar ta Anambra, ya bayyana hakan a yau asabar ta hannun kakakin sa Ibrahim Uma
Daga cikin matakan da yace akwai bukatar a dauka don shawo kan matsalolin da Afrika ke ciki akwai kakkabe talauci, magance rashin adalci, ta dakile nuna wariya a tsakanin al’umm
Sannan yace kaso 50 cikin dari na masu fama da talauci a duniya yan nahiyar Africa ne, inda ya kara da cewa kaso 60 cikin dari na al’ummar kasashen Najeriya da Congo suna yin rayuwa a cikin kuncin talauci
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
