Connect with us

News

Gobarar Tankar Mai Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Sama Da Mutum 100 A Jigawa 

Published

on

FB IMG 1729072611942

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Hukumomi a Jigawa sun tabbatar da mutuwar kusan mutum 100 sakamakon gobarar da wata tankar mai ta yi a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Advertisement

Tankar ta tashi ne daga jihar Kano a kan hanyarta ta zuwa garin Nguru na jihar Yobe amma ta yi hatsari a yankin ƙaramar hukumar Taura ranar Talata da daddare.

Tsadar ƙwai da nama sun sanya al’umma neman mafita da roƙon gwamnati

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa DSP Lawan Shiisu Adam ya ce mutum aƙalla 94 ne suka mutu sannan fiye da 50 suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi bayan tankar man ta faɗi.

Advertisement

Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne yayin da mutane suke rige-rigen kwasar fetur daga cikin tankar, abin da ya haddasa gobara.

DSP Lawan Shiisu Adam ya ce: “A jiya Talata da misalin 11:30 na dare muka samu labarin hatsarin wata tanka da ta taso daga Kano za ta je Nguru. A lokacin da ta zo Taura kusa da Khadija University, sai motar ta ƙwace daga hannun direban hakan ya sa tankar ta faɗi.

Advertisement

“Sai mai ya riƙa malala yana shiga magudanar ruwa da kwatoci. Wannan dalili ne ya sa mutane sun ga banza ta faɗi suka fito suna ɗiban mai. A lokacin ne wuta ta tashi. A nan-take an samu mutum 94 da wuta ta ƙone su ƙurmus, sai kuma mutum 50 da aka ɗiba aka kai su asibitin garin Ringim inda suke karbar magani,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Wasu rahotanni dai su ce mutanen da suka mutu sun zarta 150, kuma ana sa rai adadin zai ƙaru.

Advertisement

Ana yawan fuskantar hatsarin mota a Nijeriya sakamakon tuƙin ganganci da rashin bin dokoki lamarin da kan haddasa asarar rayuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending