Connect with us

News

Naushe Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Mai Rabon Faɗa 

Published

on

Naushe Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Mai Rabon Faɗa 

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Wani mai suna Markus Dali mazaunin Sina Kwande a karamar hukumar Michika a jihar Adamawa ya rasa ransa yayin da ya ke kokarin rabon faɗa tsakanin wasu mutane biyu.

Advertisement

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta lokacin da Dali ya shiga tsakanin Barka Yama da Alex Z. Tari domin ya raba su faɗa.

Gobarar Tankar Mai Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Sama Da Mutum 100 A Jigawa 

Daily Trust ta tattaro cewa Barka ya kawo naushi sai ya samu Dali wanda hakan ya sa ya fadi sumamme, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa a asibiti.

Advertisement

An kama wanda ake zargin mai shekaru 32, Barka, kuma an tuhume shi da laifin kisan kai a karkashin sashe na 191 na kundin laifuffuka.

A wata kotun majistare da ke Yola, dan sanda mai shigar da kara, ASP Francis Audu, ya ba da labarin yadda lamarin ya faru, inda ya bayyana cewa Dali ya yi kokarin raba masu fadan biyu amma Barka ya yi masa mugun rauni.

Advertisement

Alkalin Kotun, Majistare Muhammed Njidda ya bayar da umarnin tsare Barka a gidan gyaran hali, har zuwa lokacin da ake jiran shawarar shari’a daga ma’aikatar karɓar kararrakin jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending