News
Ana Tsaka Da Jiran Dawowar Shugaba Tinubu Najeriya Shettima Zai Dage Zuwa Kasar Sweden
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotanni na nuni da cewar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zai dage zuwa kasar Sweden a wata ziyarar kwanaki 2 da zai yi game da hulɗar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu.
Stanley Nkwocha, kakakin mataimakin shugaban kasar, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ziyarar an yi ta ne a maimakon shugaba Tinubu.
“Ana sa ran mataimakin shugaban kasa Kashim zai dawo kasa Najeriya a ranar Asabar. Yayin da ya shirya dagewa zuwa kasar Sweden, Ziyarar ta sa zai samu Zaman tattaunawa mai zurfi da manyan jami’an gwamnatin kasa Swidin , ciki har da Gimbiya Victoria ta Ƙasar da kuma firaministan” .Cewar Stanley.
Kakakin ya ce yayin ziyarar mataimakin shugaban kasar zai yi amfani da hakan ne don gano damammakin karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Sweden a fannonin ICT, kirkire-kirkire, ilimi, na’urar zamani, sufuri mai dorewa, hakar ma’adinai, da kuma noma.
Haka kuma zai gana da manyan masu ruwa da tsaki a bangaren gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.
Mataimakin shugaban kasar zai kuma gana da Norrsken, wani mai saka hannun jari mai tasiri a Stockholm, wanda kwanan nan ya ƙaddamar da Norrsken22, asusun saka hannun jari na fasaha na dala miliyan 205 don Afirka.
Haka kuma ana sa ran Kashim zai zakulo tare da hango goben tattalin arzikin Najeriya da kuma sauye-sauyen da gwamnatin ke yi domin samar da yanayin da zai dace da kasuwanci a Najeriya ga masu zuba jari.”
Wannan tafiya ta mataimakin shugaban ƙasa ta zo dai dai da karewar Hutun mako biyu da shugaba Bola Tinubu ya tafi zuwa kasar Birtaniya a ranar 2 ga watan Oktoba, 2024
-
News6 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
