Connect with us

News

Tankar Man Fetur Ta Sake Fashewa Ya Yin  Da Mutane Suka Jikkata Gidaje Da Motoci Suka Kone

Published

on

Gidaje Da Motoci sun Kone, Mutane Sun Jikkata Bayan Fashewar Tankar Man Fetur A Ogun
Tankar man fetur ta kama da wuta ne a wani gari da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Wata tankar man fetur da ta yi hatsari da sanyin safiyar Laraba ta kona gidaje da motoci tare da jikkata wasu mutane biyu a garin Ibafo da ke karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun a ranar Laraba.

Advertisement

LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa, tankar man fetur ta kama da wuta ne a wani gari da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

Ana Tsaka Da Jiran Dawowar Shugaba Tinubu Najeriya Shettima Zai Dage Zuwa Kasar Sweden

Shedun gani da ido sun ce, tayar tankar ce ta fashe, wanda hakan ya yi sanadin faduwar motar .

Advertisement

Tankar ta fashe bayan faduwa inda ta lalata gidaje da ababen hawa da ke kusa da wurin, inji wani ganau.

Akalla motoci biyar da suka hada da manyan motoci sun lalace yayin da wasu mutane biyu suka samu raunuka.

Advertisement

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a Abeokuta, Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi, ya ce, ba a samu asarar rai ba a lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending