News
Kungiyar Direbobin Tankar Dakon Fetur Na Barazanar Ballewa Daga Kungiyar NUPENG
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kungiyar direbobin tankokin mai karkashin kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, tayi barazanar ficewa daga kungiyar NUPENG.
Kungiyar direbobin ta ce za ta fice daga kungiyar idan shugaban NUPENG na kasa, Williams Akporeha, da babban sakatarenta, Olawale Afolabi, suka gaza sauka daga kan mukamansu.
Ma’aikatan Shari’a dake Zanga-Zanga Sun Garkame Kofar Shiga Babbar Kotun Osun
Direbobin tankar sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a Abuja tare da sanya hannun Gbenga Olawale da Adekunle Rufa’I dake shugabantar Depo na Ibadan.
Sanarwar ta ce direbobin sun gudanar da zanga-zangar a fadin kasarnan, inda suka nuna kwalaye da ganye a gaban manyan motocinsu, sannan kuma sun gargadi kungiyar ta NUPENG da ‘yan sanda kan tsoma baki da cin zarafin shugabanninsu.
A wani labarin kuma Ma’aikatan Shari’a dake Zanga-Zanga Sun Garkame Kofar Shiga Babbar Kotun Osun
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta ce an gano gawawwakin mutum huɗu da wani hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja kwana hudu bayan faruwar lamarin.
Shugaban sashen yaɗa labarai da ayyuka na musamman na hukumar Ibrahim Audu ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Jaridar Daily Trust dai ta ruwaito cewa wani jirgin ruwa ɗauke da mutum 34 ya kife a yammacin ranar Alhamis, inda mutum 10 suka mutu, yayin da aka ceto 24.
Fasinjojin waɗanda akasari ƴan kasuwa ne, sun haɗa da maza 20 da mata 14, daga cikinsu akwai yara mata takwas da manya mata shida.
Sai kuma yara maza biyu da manya maza 18.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
