News
Ma’aikatan Shari’a dake Zanga-Zanga Sun Garkame Kofar Shiga Babbar Kotun Osun
DAGA MUHAMMAD ZAHRADDIN
Mambobin kungiyar ma’aikatan shari’a a jihar Osun a ranar Litinin sun kulle kofar shiga babbar kotun jihar Osun da ke Osogbo domin nuna adawa da babban alkalin alkalan kotun, Adepele Ojo da gudanar da harkokin shari’a a jihar.
Ma’aikatan da suka gudanar da zanga-zangar karkashin jagorancin Mista Gbenga Eludire, sun hana shiga harabar kotun.
Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Sun Bukaci A Kauracewa Shiga Haramtaccen taro, Ko Zanga-Zanga
Masu zanga-zangar suna dauke da alluna masu dauke da rubuce-rubuce irin su ‘Ma’aikatan Shari’a sun fi cancanta,’ ‘Mun gaji da zalunci da tabarbarewar al’amura, da kuma ‘dakatar da ma’aikatan shari’a ba bisa ka’ida ba ba tare da neman hukumar kula da shari’a ba, haramun ne, da dai sauransu.
Daily Post ta ruwaito cewa Sannan sun zargi Ojo da kin biyan albashi da alawus alawus na ma’aikata a cikin shekaru uku da suka gabata.
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Sun Bukaci A Kauracewa Shiga Haramtaccen taro, Ko Zanga-Zanga
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na soke zaɓensa a matsayin koma baya na wucin-gadi, wanda ba zai hana shi mayar da jihar kan turbar hadin kai da zaman lafiya da ci gaba ba.
Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a dawo da nasarar da al’ummar jihar suka ba shi, domin ya umurci tawagarsa ta lauyoyi su shigar da ƙara a kotun ƙoli.
Mutfwang, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya buƙaci al’ummar jihar da magoya bayan jam’iyyar PDP da su kwantar da hankalinsu, ya kuma ba su tabbacin za a martaba da kare zaɓin al’umma.
Ya kara jaddada aniyarsa ta bin doka da oda, ya kuma tabbatar wa jama’a cewa za a cimma haske a karshe, domin ya yi imani da adalcin ɓangaren shari’a da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.
Mutfwang ya buƙaci magoya bayansa, da kuma ‘yan jihar da su tabbatar da doka da oda.
Ya kuma tabbatar da cewa jihar za ta yi nasara inda ya sake tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da yi wa jihar hidima da kwazo da gaskiya.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
