Connect with us

News

Rundunar Yan Sandan  Jihar Kano Sun Bukaci A Kauracewa  Shiga Haramtaccen taro, Ko Zanga-Zanga 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi kira ga al’umma su kwantar da hankulansu, su kaucewa shiga duk wani nau’i na haramtaccen taro, ko zanga-zanga, ko tattaki da ka iya haifar da tarzoma.

Advertisement

Rundunar, a cikin wata sanarwa da kakakinta, Haruna Kaiyawa, ya fitar, ta ce sahihin bayanai da ke hannunta, sun ce wasu kungiyoyin magoya bayan wata jam’iyyar siyasa na amfani da kafafen yada sada zumunta, suna tara jama’a da shirin fitowa kan tituna domin nuna adawa da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Mutum 547,774 Ne Suka Neman Aikin Dan Sanda A Nageriya

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan, Mohammed Usaini Gumel, ya yi kira ga daukacin al’ummar da su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani nau’i na taro, ko zanga-zanga, ko Tattaki.

Advertisement

Ya ce duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a Jihar za a kama shi kuma zai fuskanci fushin doka.

A wani labarin kuma Mutum 547,774 Ne Suka Neman Aikin Dan Sanda A Nageriya

Advertisement

Tsohon Firaministan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Augustin Matata Ponyo, ya janye daga zaben shugaban kasar da za a yi a watan gobe.

Ya ce yanzu zai marawa Moïse Katumbi, hamshakin attajiri kuma tsohon gwamnan yankin Katanga baya.

Advertisement

Wakilan manyan jam’iyyun adawa na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun gudanar da tattaunawa a farkon makon nan kan yadda za a tabbatar da gudanar da zaɓe cikin adalci, da kuma gudanar da bincike kan yiwuwar ɗan takara na hadin gwiwa da zai kalubalanci shugaba Felix Tshisekedi.

Ponyo ya ce ya yi imanin sauran ‘yan takarar jam’iyyar adawa za su bi sahunsa na janyewa don goyon bayan Katumbi.

Advertisement

Dukansu sun yi aiki a zamanin tsohon shugaban kasa Joseph Kabila – Ponyo a matsayin firaminista sama da shekaru hudu da Katumbi a matsayin gwamnan lardin Katanga na tsawon shekaru tara.

Tshisekedi, wanda ke neman wa’adi na biyu, na cikin ‘yan takara da dama da suka ƙaddamar da yakin neman zabensu a hukumance ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending