Connect with us

Business

Za Mu Janye Ƙarar Da Mu Shigar A Gaban kotu akan NNPCL  Da Sauransu – Masana’antar Dangote

Published

on

download

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Masana’antar Dangote ta yi karin haske kan rahotannin da suka shafi ƙarar da aka shigar kan Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) da wasu kamfanoni biyar kan shigo da man fetur.

Advertisement

Waɗannan kamfanoni biyar sune Aym Shafa Limited, A. A. Rano Limited, T. Time Petroleum Limited, 2015 Petroleum Limited da Matrix Petroleum Services Limited.

Matatar Dangote Ta Nemi Kotu Ta Soke Lasisin Shigo Da Mai Na NNPC, Matrix A.A. Rano, Da Wasu Kamfanoni Guda Huɗu 

Masana’antar Dangote, a cikin ƙarar da aka shigar mai lamba: ta FHC/ABJ/CS/1324/2024, wacce Lauya Ogwu Onoja, SAN, ya shigar gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo, ta kai ƙarar Hukumar Kula da Man Fetur ta da Hukumar (NMDPRA) da NNPCL a matsayin masu ƙara na 1 da 2.

Advertisement

Haka kuma, an bayyana Aym Shafa Limited, A. A. Rano Limited, T. Time Petroleum Limited, 2015 Petroleum Limited, da Matrix Petroleum Services Limited a matsayin masu ƙara na 3 zuwa na 7 a cikin sammacin da aka sakawa kwanan wata 6 ga Satumba.

Kamfanin Dangote ya kuma nemi a biya shi diyyar Naira biliyan 100 tare da bukata akan a janye lasisin shigo da kaya ga NNPCL da kamfanoni biyar.

Advertisement

Dangote ya ce kayan nan su ne Man Dizal da Man Jirgin Sama (Jet Fuel), waɗanda ake shigowa da su cikin Najeriya duk da cewa Masana’antar Dangote tana samar da AGO da Jet-A1 da ya wuce bukatar yau da kullum a Najeriya.

Mai shigar da ƙarar ya roki kotu da ta bayyana cewa NMDPRA ta keta doka shashi na 317(8) da shashi na (9) na Dokar Masana’antar Man Fetur ta Najeriya (PIA) ta hanyar ba da lasisi don shigo da kayayyakin man fetur ba bisa ka’ida ba.

Advertisement

Sai dai Anthony Chiejina, Babban Jami’in Dangote ya bayyana cewa wannan ƙarar ba sabon abu ba ne.

“Wannan tsohon shigar da kara ne da ya fara tun a watan Yuni kuma ya kai ga shigar da kara a ranar 6 ga Satumba, 2024.”

Advertisement

Bangarorin suna tattaunawa tun bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu kan shirin sayar da Danyen Mai da Kayayyakin Mai da aka tace wanda ake sayar da shi a farshin Naira, wanda Majalisar Zartaswa ta Ƙasa (FEC) ta amince da shi.

Mun samu gagarumin cigaba a wannan fannin kuma abubuwan da suka faru sun riga wannan cigaban.

Advertisement

Babu wata bangare da aka isar wa da takardun kotu, kuma babu niyyar yin hakan. Mun yarda da dakatar da shari’ar a yanzu

“Yana da mahimmanci a jaddada cewa babu wata umarni da aka bayar kuma babu wata illa ga kowanne bangare. da zarar lamarin ya zo a watan Janairu 2025, za mu janye shari’ar daga kotu gaba ɗaya.”inji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending