Business
Kungiyar Dillalan Mai IPMAN Da Matatar Dangote, Sun Cimma Yarjejeniyar Cinikayyar Mai Kai Tsaye
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya IPMAN, ta kulla yarjejeniya da matatar Dangote da zata ba yan kasuwar damar sayen mai kai tsaye.
Shugaban IPMAN na kasa Abubakar Garima wanda ya sanar da hakan a Abuja, bayan kammala taron shugabannin kungiyar, yace an samu wannan ci gaba ne bayan tattaunawa tsakanin bangarorin biyu
Duk Ma’aikacin Da Bai Yi Rijistar Jiha Ba ,Ba Za Ta Ba Shi Albashi Ba —Gwamnati
Abubakar Girima ya yi amannar cewa wannan yarjejeniya zata kara taimakawa wajen samun wadataccen mai a fadin kasar
Dangane da farashi kuwa, Shugaban na IPMAN ya nuna kwarin gwuiwar cewa tattaunawar da suke yi da matatar Dangote za ta haifar da da mai ido.. .