News
Shugaba Tinubu Ya Bar Kasar Brazil Bayan Taron G20 Daya Halarta A Makon Jiya
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Shugaban Kasa Bola Tinubu da mai dakinsa Oluremi suna kan hanyar dawowa Nageriya bayan halartar taron shugabannin kasashen masu karfin tatttalin arziki na G20 karo karo na 19 wanda ya gudana a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.
Tinubu zai sauka a filin jirgi na Nnamdi Azikiwe dake Abuja kamar yaddda jaridar Vanguard ta rawaito.
Tun da fari shugaba Tinubu ya halarci taron shugabannin kasashen G20, inda ya amince da kawancen duniya na yaki da yunwa da fatara, wanda ya ce yana da matukar muhimmanci ga Nageriya.
A taron daya Halarta Tinubu ya gana da shugabar asusun ba da lamuni na duniya Kristalina Georgieva, wadda ta yabawa gwamnatinsa bisa tsare tsaren da takeyi a fannin Noma da Kiwo domin sauye-sauyen tattalin arzikin Nageriya.
Kamfanin dillancin Labarai Na Ƙasa (NAN ) ya rawaito shugaba Tinubu ya rattaba hannun zuba jari na Naira biliyan 2.5 tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin samar da nama na JBS S.A.
