Connect with us

News

Dan Uwan Kwankwaso Ya Maka Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf A Gaban Kotu

Published

on

1732375398562

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rikicin fili a jihar Kano ya dauki sabon salo bayan da Garba Kwankwaso, kani ga tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ya maka Gwamnan Abba Kabir Yusuf a gaban Kotu

Advertisement

A cikin Shari’ar da Garba Kwankwaso ya shigar ya bukaci a shiga tsakaninsa da Gwamnatin Abba  domin hana gwamnan  daukar wani mataki akan wani fili da aka jima ana rikici akansa.

 

Advertisement

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa tun da fari asalin filin na Kwankwaso ne daya baiwa wani kamfani mai suna WAECO, amma sai tsohon gwamnan Abdullahi Ganduje ya kwace.

Daga baya sai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jiha ta tabbatar da kwace filin, wanda ya ke a unguwar Kwankwasiyya City., bisa hujjar cewa Kamfanin  WAECO bashida wata cikakkiyar rijista.

Advertisement

 

Daga nan ne sai Ganduje ya dawo da kasuwar yan magani cikin wani bangare na filin kafin daga bisani  a tashesu.

Advertisement

 

Itama sabuwar gwamnatin Abba da’ta zo sai taƙi maidawa kamfanin WAECO filin, shine Garba Kwankwaso ya shigar da kara a gaban Kotu.

Advertisement

 

A umarnin da ya bayar, Mai Shari’a Usman Na’abba ya bada umarnin hana taba filin ga gwamnati sannan ya dage sauraren koken zuwa 27 ga watan Nuwamba.

Advertisement

Cikin mutanan da Garba Kwankwaso ya shigar da  Kara sun hadar da kwamishinan filaye da tsare-tsare na jihar Kano da Shugaban Hukumar Kula da tsare-tsare da cigaban Birane ta Jihar Kano, KNUPDA da Babban Lauyan Jihar Kano da mutun guda wanda ba’a bayyyanaba.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending