Connect with us

News

Shugaba Tinubu Zai Saka Hannun Jari A Fannin Noma Da Kiwo Don Magan Ce Matsalar Manoma Da Makiyaya

Published

on

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na magance rikicin manoma da makiyaya ta hanyar saka jari don bunkasar bangarorin biyu a Najeriya.

Advertisement

Tinubu ya bada tabbbacin hakan ne a wani jawabi da yayi a wani taron hadin gwiwa na manyan kamfanunuwan sarrafa nama na duniya wanda ya gudana a birnin Janeiro na kasar Brazil a ranar Alhamis kamar Yadda Jaridar Punch ta rawaito.

 

Advertisement

Cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma’a ya ce shirin ya yi daidai da tsarukan Bola Tinubu na sauya fasalin noma don ci gaban tattalin arziki.

Tinubu ya bayyana hadin gwiwar a matsayin wani gagarumin mataki na kawar da yunwa da rage radadin talauci, da bunkasa tattalin arziki a kasar .

Advertisement

“Abin da muke yi a yanzu shi ne magan ce matsalar da ta addabi Al’umma a yankin Afirka da tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya wanda ya yi sanadin asarar rayuka da zubar da jini.

A cewar sa akwai hanyar zamani da zata don magance waɗannan matsalolin da samar da ingantaccen tattalin arziki daga ga manoma da makiyaya.

Advertisement

Itama Kasar Brazil hadin gwiwa da JBS.S.A sun nuna farin cikin yin aiki tare da Najeriya don bunkasa masana’antar kiwon dabbobi.

Tawagar ta Najeriyar ta samu rakiyar karamin ministan noma da samar da abinci, Aliyu Sabi Abdullahi, mataimakin shugaban kwamitin gyaran dabbobi na fadar shugaban kasa, Farfesa Attahiru Jega, sakataren kwamitin Farfesa Mohammed Kuta Yahya, da shugabar hukumar bunkasa zuba jari ta Najeriya, Aisha Rimi. .

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending