News
Gwamnatin Tarayyya Za’ta Tsayar Da Matsaya Akan Samar Da Yan Sandan Jihohi
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
A sati mai zuwa ne Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni za su tsayar da matsaya game da samar da ƴan sandan jihohi.
Gwamnan Jihar Bayelsa, Duoye Diri ne bayyana hakan ga manema labarai a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja, bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (NEC).
Ya ce, Majalisar ta bai wa jihohin Adamawa da Kebbi da Kwara da kuma Abuja mako guda (28 ga watan Nuwamba) su gabatar da matsayarsu game da lamarin.
Diri ya ce a yayin zaman majalisar na mako mai zuwa ne, za a cimma matsaya akan kafa yan Sandan Jihohin.
A ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar nan ne Gwamnatin Tarayya tare da jihohin ƙasar suka fara maganar samar da ƴan sandan jihohi yayin wani zama na gaggawa tsakanin Shugaba Tinubu da gwamnonin a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Ministan Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris ya ce ana cigaba da bin hanyoyin da suka dace tare da shigo da masu-ruwa-da-tsaki don tabbatar inganci game da batun wanda a yanzu haka ake jiran rahoton sauran jihohi huɗu don cimma matsaya.
