News
Atiku Abubakar : Dasa Hannun Majalisun Nageriya Wajen Sanya Al’umma Shiga Cikin Mawuyacin Hali
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya ce yawaitar ciyo basussuka da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ke yi zai ƙara jefa tattalin arzikin Najeriya cikin ƙunci.
Tsohon ɗantakarar na PDP ya kuma soki yadda majalisar dokoki ke amincewa da buƙatar ciyo basussukan, waɗanda a cewarsa suke ƙara jefa ƙasar cikin ƙangin bashi.
Atiku ya bayyana haka ne a wani rubuta da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce, “rahoton da bankin duniya ya fitar kwanan nan, wanda ke nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku da ta fi cin bashi daga hukumomin kuɗi na duniya abin damuwa ne.
“Rahoton ya fito ne a daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ta aike da wani buƙatar sake ciyo wani bashin na naira triliyan 1.7 saboda cike giɓin kasafin kuɗin 2024.
Abin da zai ƙara ɗaga hankali a game da bashin ma shi ne kasancewarar a kasafin kuɗin, an kasafta darajar dala ɗaya a kan naira 800, alhali yanzu dala ta kai naira 1,700.”
Ya ƙara da cewa Najeriya na ƙara nutsewa a cikin bashi, “sannan majalisar dokoki suna taimakawa Tinubu ya bayyana a watan Yuli cewa hukumar tattara haraji da kwastam sun tara kuɗin shiga da ba a taɓa tarawa ba. To me ya sa ake cin bashin? akwai wani abu da suke ɓoyewa ƴan Najeriya.”
Atiku ya ƙara da cewa yawan cin bashin yana ƙara takurawa tattalin arzikin.
Jaridar Inda ranka ta rawaito cewa idan gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta ciwo wannnan bashin Dala Biliyon 2.2 ya zamana anabin Nageriya Naira Tiriliyan 138.
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gaji bashin Naira Tiriliyan 87.3 daya gada a gwamnatin baya inda shima a cikin kasa da watanni 20 da yayi akan mulki ya ciyo bashin Naira Naira Tiriliyan 50.7 idan aka hada da wanda majalisssar ta amincemasa a jiya Alhamis.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
