News
Har Yanzu Amb. Ibrahim Waiya Ne Shugaban Gamayyar Kungiyoyi Masu Zaman Kansu A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Har yanzu Amb. Ibrahim Waiya ne shugaban gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kano.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar da Mataimaki na Musamman kan harkokin yaɗa labarai Bashir A Bashir ya turawa da Jaridar INDA RANKA
Za A Hana Yara Ƴan Ƙasa Da Shekara 16 Hawa Instagram da TikTok
Sanarwar ta kara da cewa “Wannan sanarwar data fita mai ɗauke da sa hannun sakataren kwamitin amintattu su sani cewa a dokance basu da hurumi na tsige mamba a ƙungiya balle shugaba.
Muna tabbatar da cewa masu shirin tada wannan tarzoma ba don komai suke ba, sai don wani kuɗiri na ƙashin kansu, wanda ba cigaba ne ga al’ummar jihar Kano ba.
A saboda haka muna kira ga mambobin gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kano da suyi fatali da wannan sanarwar tare da jiran me kotu zata faɗa a mako mai zuwa.
A ƙarshe muna ƙara haƙurƙuntar da mambobin KCSF musamman masu kishin jihar Kano na tabbatar da samun Nasara a gaban kotu.
