Connect with us

News

Asibitin Kwararru Na Best Choice Ya Rage Kaso 30 Cikin 100 A Ayyukan Kula Da Hakora

Published

on

Asibitin Kwararru Na Best Choice Ya Rage Kaso 30 Cikin 100 A Ayyukan Kula Da Hakora

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A wani bangare na tausaya wa da kyautatawa al’umma da shugaban asibitin Best Choice Alh Auwal Lawal yayi ya bayyana rage kaso 30 cikin 100 na aikin kula da aikin hakora, asibitin a wata tattaunawarsa da jaridar Alfijir labarai

Advertisement

Lawan ya jaddada cewa, sabon sashin kula da hakoran zai duba mara sa lafiya ne a kan wannan ragi tare da ba su shawarwari duba da yanayin da ake ciki na sanyi

Asibitin Best Choice Ya Kaddamar Da Sabuwar Na’urar Jarirai Ta (Jaundice) Irinta Ta Farko A Arewacin Najeriya

Daga nan Auwal ya jaddada bukatar dake akwai ga duk wadanda ke fama da matsalolin hakora cewa, asibitin yayi tanadin abubuwan da suka dace game da ƙwararrun likitocin haƙora da suka goge tsawon shekaru, da kuma isassun kayan aikin haƙora na zamani.

Advertisement

Ya jaddada kudirinsu na share hawayen marasa lafiya inda ya bukace su da kada su yi sanya wajan cin gajiyar wannan tagomashi na ragi da aka samar don kula da lafiyar baki da ta hakori.

Asibitin Kwararru Na Best Choice Ya Rage Kaso 30 Cikin 100 A Ayyukan Kula Da Hak

Idan za a iya tunawa, asibitin ya koma babbar helkwatarsa ta dindindin dake shatale-talen Tal’udu kusa da Kwalejin Bashir El-rayya, dake kan titin Aminu Kano anan birnin Dabo.

Advertisement

Shugaban Asibitin Best Choice yasamu lambar yabo ta fitaccen Jakadan Zaman Lafiya Na Duniya

Ya kara da cewar baya ga ficen da suka yi a fannin kula da mafitsara, asibitin na aiwatar da muhimman ayyukan da suka hada da jinyar kananan yara (Paediatrics), tiyata (surgery), kula da masu tabin hanka( psychiatry), bangaren hakora (Dentals), gashin kashi ( physiotherapy) sashin kula da cutukan mata (Gynaecology) da bangaren masu kula da masu ciki da haihuwa, bangaren fata (dermatology), manyan dakin gwaje-gwaje, kantin magani, da sashin kula da jarirai.

Lawan ya tabbatar da cewa asibitin cike yake da na’urorin kiwon lafiya na zamani irin na kasashen duniya, ga kuma tsayayyiyar wutar lantarki 24-7.

Advertisement

Hakazalika asibitin bashi da wani reshe ciki ko wajen Kano, mazauninsa na dindindin na shatale-talen Tal’udu kusa da Kwalejin Bashir El-rayya, dake kan titin Aminu Kano anan birnin Dabo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending