News
A Gobe Laraba Shugaba Tinubu Zai Yi Tafiya Zuwa Faransa kwanaki Hudu 4 Da Dawowarsa Daga Kasar Barazil
A gobe Laraba ne shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Abuja domin fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Faransa bayan amsa gayyatar da Emmanuel Macron shugaban kasar Faransa ya yi .
Ziyarar wadda za ta mayar da hankali kan karfafa dangantakar siyasa da tattalin arziki, da al’adu da samar da karin damammaki na hadin gwiwa, musamman a fannin noma, tsaro, ilimi, kiwon lafiya, harkar makamashi, ci gaban matasa da ayyukan yi da kirkire-kirkire.
A taron ana kyautata zaton cewa, za’a samar da gagarumar nasara ga Nijeriya kamar Yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu da mai dakinsa, Sanata Oluremi Tinubu, za su isa kasar a ranar Alhamis a gidan tarihi na sojojin Faransa, ‘Les Invalides da Palais de l’Élysée,’ mai shekaru 350 wanda Macron da matarsa, Brigitte za su tarbe su, wanda daga bisani za su shiga cikin tattaunawar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, shugaba Tinubu zai sami rakiyar manyan ma’aikatan gwamnatin a wannan tafiya.
