News
Kungiyar MATAN ta Kaddamar da raban Shinkafar Gwamnatin Tarayya Kan N40,000 A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Yan kasuwa ta kasa watau Market Traders Association of Nigeriarashin jihar kano ta sanar da cewa yan Kungiyar su gajiyar shirin Gwamnatin Tarayya na karya farashin shinkafa, inda aka sayar da kowane buhu a kan Naira 40,000.
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da shinkafarta kan Naira dubu 40,000, saɓanin yadda farashinta yake a kasuwa na Naira dubu 80 da ’yan kai.
Da yake bayyana matakan da Kungiyar ɗauka Dr Sadiq Umaru Kushi Mai Magana da yawan Kungiyar ya ce domin rage wa ƴan Najeriya nauyin tattalin arziƙi a sakamakon cire tallafin man fetur da sauran tsare-tsaren sauye-sauyen kuɗaɗe, Umaru ya yi nuni da ƙoƙarin rage wa mutane ƙunci da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi.
“Ana hasashen cewa gidaje 1000 ne suka ci gajiyar shirin sayar da shankafar akan Naira 40000 kai-tsaye,” in ji shi, yana mai jaddada yawan waɗanda suka amfana da shirin.
Kara da cewa, babban maƙasudin ɗaukar wannan matakin shi ne samar da walwala ga talakan Najeriya wanda ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa.
Kazalika, ya bayyana cewa za a tabbatar cewa, babu wanda ya sayar da buhun shinkafar sama da farashin Naira dubu 40,000.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
