Connect with us

Labarai

Manyan Motocin Daukar Kaya Za Su Daina Shigowa Kano Da Rana — Gwamnatin Kano

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa manyan motocin daukar kaya za su daina shigowa cikin birnin Kano da rana, domin rage cunkoson ababen hawa da kuma bunkasa tsaro a jihar .

Kwamishinan Sufuri na Jihar Muhammad Ibrahim Diggol, ne ya bayyana hakan, yayin tattaunawarsa da Kafar yada Labarai ta HIKIMA RADIYO, a shirin su mai suna HANNU DAYA.

Babu Wata Doka Data Baiwa Yan Sanda Damar Haska Fuskar Wanda Ake Zargi Da Aikata Laifi —Masanin Harkokin Shari’a

Wannan mataki yana daga cikin kudurorin gwamnati na tabbatar da kyakkyawan tsarin sufuri a jihar.

Wannan dokar za ta fara aiki nan ba da jimawa ba, inda aka tsayar da lokacin da motocin daukar kaya za su iya shigowa da kuma fita daga birnin.

Ana sa ran wannan tsari zai rage wahalhalun tafiye-tafiye ga ‘yan gari da kuma kare muhalli daga matsalolin da cunkoso ke haifarwa.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending