Connect with us

News

Babu Wata Doka Data Baiwa Yan Sanda Damar Haska Fuskar Wanda Ake Zargi Da Aikata Laifi —Masanin Harkokin Shari’a

Published

on

Doka

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wani masanin harkokin shari’a kuma Malami a tsangayar koyar da harkokin Shari’a a Jami’ar Bayero dake Kano ya ce, kuskure ne babba yadda jami’an tsaro ke haska fuskokin mutanan da ake zargi da sunan sun aikata Laifi ba tare da an tabbatar da abin da ake zarginsu da shi ba.

Advertisement

Barriester Nuhu Isa Idris ya bayyana hakan ne yayin taron karawa juna Sani da cibiyar cigaban al’umma da wayar da Kai a nan Kano CDE ta shiryawa manema labarai a jihar.

Gwamnatin Tarayya Ta Kori Ma’aikata Masu Digiri Ɗan Kwatano Da Togo

“A matsayina na wanda ya shafe sama da Shekaru 20 Ina aikin lauya kuma Ina koyar da dalibai harkokin Shari’a, har yanzu banga wata doka da ta baiwa jami’an tsaro damar yiwa mai laifi bidiyo kuma har a yada a kafafen sada zumunta ba”. A cewar . Nuhu Musa

Advertisement

Ya Kuma ce, idan har aka nuna fuskar Wanda ake zargi Kuma daga baya aka gano Bashi da Laifi an cutar da shi da Kuma iyalansa baki Daya.

“A doka duk wanda ba alƙali ba ne ya yanke masa hukunci ba dace a kirawo shi da mai laifi ba, daga lokacin da jami’an tsaro suka kama shi ko aka kawo shi sunansa wanda ake zargi, idan kuma aka gabatar da shi a Kotu sunansa wanda ake tuhuma, ba zai zama mai laifi ba har sai lokacin da alkali ya tabbatar da cewa an kama shi da laifin da ake tuhumasa”. Inji Dr. Nuhu Musa Idris

Advertisement

Ya bukaci jami’an tsaro da su tabbatar suna gudanar da aiyukansu akan dokokin da suka kafa su da kuma dokokin Najeriya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending