Connect with us

News

Kungiyar ASUU Ta Gargadi Gwamnatin Tarayya Akan TETFUND 

Published

on

Jami'oi Masu Zaman Kansu KE Rabon First Class Ga DalibansuGaskiya Akwai Lauje Cikin Na ASUU

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ƙungiyar malaman jami’a ASUU, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta guji yin duk wasu abubuwa da za su kassara asusun bayar da tallafi ga manyan makarantu wato TETFUND.

Advertisement

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da tashar talabijin ta Channels, inda ya yi zargin cewa matakin, “zai kassara jami’o’in Najeriya, da kuma bautar da yaran talakawan Najeriya.”

Manyan Motocin Daukar Kaya Za Su Daina Shigowa Kano Da Rana — Gwamnatin Kano

“Hanyar jami’o’in Najeriya suke samun kuɗi ita ce TETFund, don haka idan ka taɗile ta, kamar ka taɗiye jami’o’in Najeriya ne,” in ji shi.

Advertisement

Shugaban na ASUU ya ce ƙudurorin harajin da Tinubu ya kawo, ba a yi shawara da masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi ba kafin a tura majalisa.

“Gwagwarmayar ASUU ce ta samar da TETFund. Bai kamata a yi ƙudurorin haraji ba, ba tare da an nemi shawarar ASUU ba. Kuma ba a nemi shawarar shugabannin jami’o’i ba. Wasu ne kawai suka zauna a wani wurin suka shirya dokokin nan. Ba haka ya kamata a yi ba, musamman a mulkin dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Advertisement

Osodeke ya ce maimakon a ce za a cire kuɗaɗen da ake ba TETFund domin a inganta asusun ba ɗalibai lamuni wato NELFUND, gara a nema wa asusun na NELFUND kuɗi daga kuɗin harajin VAT

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending