News
Masu kananan masana’antu sun gudanar da sallar Alkunutu saboda rashin lantarki

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Masu kananan sana’o’i da matsakaitan sana’o’i da ke Dakata a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano sun gudanar da taron addu’o’i na musamman bayan shafe kwanaki 70 basu da wutar lantarki a yankin.
Rahotanni sun ce katsewar ya shafi yan Kasuwa sama da 10,000 a yankin, inda masu gudanar da aikin suka yi kiyasin hasarar miliyoyin naira.
Majalisar Dokokin Kano Na Shirin Keɓe Wa Masu Sayar Da Iskar Gas Wuri A Kano
A yayin zaman addu’o’in ‘yan kasuwar sun nuna bacin ransu, inda suka nemi taimakon Allah a kan lamarin .