Politics
Shugabar karamar Hukumar Tudun wada ta taya Daukacin Alumma murnar shigowa sabuwar shekarar 2025.

DAGA ALIYU DANBALA GWARZO.
Shugabar karamar Hukumar Tudun wada Hajiya Sa’adatu Soja tayi Fatan samun cigaba fiye da wanda aka samu a shekarar da mukayi bankwana da ita tare da Fatan samun zaman lafiya mai dorewa a fadin duniya baki daya.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da maitaimakinta na musamman ya rabawa manema labarai a safiyar wannan Rana ta Laraba.
Shugabar tace, “cikin ikon Allah da amincewar sa yau mun shiga sabuwar shekarar Miladiyya ta 2025 a lokacin da mukayi bankwana da kalandar shekarar 2024 a jiya kenan Muna rokon Allah ubangiji da wannan sabuwar shekara ta 2025 ta zamo shekarar da zamu samu cigaba fiye da na shekarar da ta wuce, mu samu zaman lafiya fiye da na shekarar data wuce, mu samu yalwar arziki fiye da na shekarar data wuce.
Takara da cewa “A wannan gabar ne nake sake rokon Allah ubangiji da ya taimaki karamar hukumar Tudunwada da al’ummar ta, ya zaunar damu lafiya, ya kawo mana duk wani cigaba da zai kara daga darajar karamar hukumar Tudun wada, Ya Allah kayi riko da hannayen mu wajan cigaba da kawo wa karamar hukuma cigaba, Allah ka dafa mana kayi riko da hannayen mu.
Amin
Daga karshe Hajiya Sa’adatu tayi kira ga Alummar karamar Hukumar Tudun wada dasu cigaba da bata hadinkai domin tacigaba da kawo managartan tsare tsaren dazasu Amfani Alumma baki daya.
Barkan mu da shigowa kalandar 01-01-2025