Politics
Na’ Bar Tafiyar Buhari Ne Sabida Ya Cutar Da Yan Najeriya Musanman Ma Talakawa – Rarara

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitaccen mawakin siyasa a Najeriya Dauda Adamu Kahutu wanda akafi sani da Rarara ya ce yabar tafiyar tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ne sabida cutar da talakawan Najeriya, bawai sabida mulkinsa yazo karsheba kamar Yadda ake yadawa.
Rarara ya ce a lokacin da Shugaba Buhari ke kokarin barin Mulki yazo da wani na sake launin Kudi da juma ajiyar kuɗi a Banki wato CHASLEES POLICY Wanda hakan yasan ya yan Najeriya shiga mawuyacin hali.
Rarara ya baiyyana na hakan ne a cikin wani shirin Siyasa Mai suna Maraicen Kura da ake gabatarwa a tashar DAN UWA RANO TV dake manhajar YouTube.
Rarara ya ce a lokacin sabida son zuciyarsa na Buhari yasa akayi chanjin kudi sabida Kada Shugaba kasa Bola Ahmad Tinubu ya sami wata damar da zai amshi mulkin Nageriya duk kuwa da yasan cewar wannann chancin kuɗi yasan da cewa Talakawa zasu sha wahala.
Talakawa sunsha wahala Matuka wasu ma sun mutu sabida san rai irin na Buhari haka zalika da dama sun taluache masanmman ma masu kana jari.