Politics
Abbas Sani Abbas Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa APC

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon Kwamishinan Raya Karkara da Cigaban Al’umma na Jihar Kano, Abbas Sani Abbas ya fice daga jam’iyyar (NNPP) zuwa Babbar jam’iyya mai Mulki ta (APC).
Abbas wanda yana daya daga cikin kwamishinoni shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke daga mukamansu a watan da ya gabata, ya bayyana sauya shekarsa a wata ziyarar da ya kai’wa wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a Kano.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karbeshi tare , da tabbatar da matakin Hon Abbas a matsayin tuna ni mai Kyau kamar Yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Jibrin ya yabawa Abbas bisa jajircewarsa na hada kai da jama’iyyar tasu tare da nuna kwarin guiwa kan yadda zai bayar da gudunmawar ci gaban jam’iyyar.
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas, da sauran shugabanni, sun rungumi Abbas Sani Abbas hannu Biyu Biyu tare da bashi tabbacin goyon baya kuma zamu hada kai don samar da makoma mai kyau ga jihar Kano da ma Najeriya Baki daya..
Ana kallon ficewar Abbas a matsayin wani gagarumin ci gaba a fagen siyasar Kano yayin da jam’iyyar APC ke ci gaba da karfafa matsayinta a jihar.