Connect with us

News

Jihar Katsina – Sojoji Sun Bukaci Yan’ Jaridu Da Su Ci Gaba Da Basu Gudunmawa Wajen Dakile Ta’addanci  

Published

on

DAGA MAHAMMAD MAHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar sojin Najeriya ta ta bukaci Yan Jaridu da su ci gaba da bayar da goyon bayansu na yaki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a fadin jihar Katsina.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Kwamandan bataliya ta 17 Brigade, Brig.-Gen. Babatunde Omopariola, ne ya yi wannan kiran a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) reshen Jihar Katsina.

Advertisement

 

Mista Omopariola ya ce ya kamata kuma a baiwa aikin jarida mahimmanci don magance matsalar rashin tsaro yadda ya kamata.

Advertisement

 

Ya ce an shirya taron ne da nufin samar da yanayi mai annashuwa na cudanya da aiki tare a tsakanin kafafen yada labarai da sojojin Najeriya.

Advertisement

 

Mista Omopariola ya kara da cewa kafafen yada labarai na taka rawar gani a kullum wajen tsara ra’ayoyin jama’a, don haka suke yin tasiri kan ayyukan soji da kuma karfafa goyon bayan jama’a yayin da suke bayyana aikace aikacen jami’ain tsaro.

Advertisement

 

Ya ce Sanya ‘yan jarida cikin tsare-tsare da gudanar da ayyukan soji zai taimaka matuka wajen duba munanan ayyukan hukumomin tsaro.

Advertisement

 

“Haka kuma ya zama wani dandali ga sojoji don nuna abokantaka da kafafen yada labarai da kuma dinke barakar da ke tsakaninsu,” in ji shi.

Advertisement

 

Kwamandan ya kuma umarci masu aikin yada labarai da su kasance masu kishin kasa a yayin gudanar da ayyukansu, ya kuma bukace su da su guji rahotannin da za su kawo cikas ga muradun kasa da tsaro.

Advertisement

 

Da yake mayar da martani, shugaban NUJ reshen jihar katsina Tukur Den-Ali, ya godewa kwamandan birgediya da hafsa bisa kyakkyawar tarba da suka yi wa ‘yan jarida.

Advertisement

 

Ya yi alkawarin cewa ’yan jarida a jihar za su rika amsa kiran da rundunar ta yi musu na fita daga cikin jajircewarsu don ba da gogewa a kafafen yada labarai a lokacin da ake bukata.

Advertisement

 

Ya kuma tabbatar wa kwamandan cewa duk wani dan jarida mai aiki a jihar zai ci gaba da hada hannu da birgediya da sauran jami’an tsaro wajen inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin.

Advertisement

 

(NAN)

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending