News
Babban Layin Samar Da Hasken Wutar Lantarki A Najeriya Ya Sauka A Karo Na Farko Cikin Sabuwar Shekarar 2025
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Babbban layin sanar da hasken wutar lantarki na Ƙasa ya sauka a Karo na Farko cikin Sabuwar Shekara 2025.
Jaridar Punch ta rawaito cewa wannan shine Karo na 13 da da aka samu na faduwar babban layin Wutar lantarki cikin watanni 13 kuma Karo na farko cikin Sabuwar Shekara.
Rahotanni na nuni da cewa faduwar da layin wutar lantarkin ya yi ta haifar da Karancin rashin wuta a fadin kasar baki daya wanda yasanya Al’umma cikin dugununun duhu.
Binciken da jaridar Punch ta yi,ya nuna cewa wutar lantarki ta ragu daga megawatts 2111. zuwa megawatts 390.20 da karfe 3 na yamma cin ranar Asabar.
DCL Hausa
Advertisements
