News
Jaridar Inda ranka Na Gayyatar Yan Uwa Da Abokan Arziƙi Zuwa Wajen Daurin Auren Abokin Aikinsu
A Madadin hukumar gudanarwa ta jaridar Inda ranka ke gayyatar Yan Uwa da Abokan arziƙi zuwa wajen daurin Auren Abokin Aikinsu wato Muhammad Muhammad Zahraddin.
Muhammad dai ya kasance daya daga ne daga cikin Shuwagabannin Jaridar Inda Ranka masu bada gudunmawa ta fuskoki daban daban domin ganin jaridar taci gaba Inganta ayyukan ta.
Haka zalika Muhammad dan gwagarmanaya ne kuma mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum wajen ganin rayuwar Matasa ta Inganta.
Haka zalika a gefe guda kuma Muhammad ya kasance dan Kasuwa da yake kasuwancinsa a kasuwar sai’da kayan masarufi ta Singa.
Za’ayi wannnan daurin Auren ne a ranar Asabar 18 January 2025 a zangon alhazai masallacin fulani dake Karamar Hukumar Nguru dake jihar Yobe da misalin karfe 11:30 na Safe.
Da fatan Allah Ubangiji ya bada ikon halarta amin summm amin.
Idan Kuma ba’a Sami damar halartaba ayiwa Ango Da Amarya Addu’a da fatan alkhairi.
