Connect with us

News

Akwai Yuwuwar Kara Kudin Man Fetur

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Man Fetur na iya tsada fiye da yadda ake sayarwa yanzu, kasancewar masu tashoshin mai sun kara farashi da kimanin kaso 4.74 cikin 100.

Advertisement

Wannan karin farashin ya biyo bayan tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, ciki har da Bonny Light na Najeriya, wanda ya tashi zuwa $80 kowanne ganga a wannan makon daga $73 a makon da ya gabata .

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Sha Alwashin Tallafawa Hukumar DMCSA Don Inganta Sashin Lafiya

DAILY POST ta rawaito cewa tuni wasu tashoshin mai, kamar Swift Depot, su ka kara farashin lodin man fetur zuwa N950 kan kowacce lita daga N907 kowanne lita. Tashar Wosbab ma ta kara farashinta zuwa N950 daga N909 kowanne lita.

Advertisement

Haka zalika, tashar Sahara ta kara farashin ta zuwa N950 kowanne lita daga N910, yayin da Shellplux ta kara zuwa N960 kowanne lita daga N908 kowanne lita.

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending