News
Cire Tallafin Man Fetur Alheri Ne Ga Gwamnatocin Jihohi .—Gwamna

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce cire tallafin man fetur alheri ne ga gwamnatocin jihohin Nijeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a Jihar Imo yayin duba wasu ayyuka, a wani ɓangare na bikin cikar shekara daya a zangon mulkinsa na biyu.
Ya ce yanzu ana samun karin kudade a asusun gwamnatocin jihohi domin ci gaban jihohinsu.
Ya ce, “Idan muka duba illolin da cire tallafin man fetur ya haifar da kuma ribar da ake samu ta fuskar ci gaban abubuwan more rayuwa, , da kuma sauƙin gudanar da gwamnati sakamakon samar da ingantattun abubuwan more rayuwa, ina ganin wannan albarka ce.
“Albarka ce kai tsaye, ba wata boyayyar alama ba ce ga gwamnatocin jihohi saboda yanzu suna samun karin kudade. Kuma gwamnatocin jihohi dole su nuna wa al’ummarsu cewa suna iya yin ayyuka domin yanzu suna samun karin kudade sakamakon cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi,” in ji shi.