Connect with us

News

Kaso 77% Na Mata Da Ke Amfani Da Kayan Shafe-shafe Na Bilicin A Duniya Yan Najeriya  —Ministan Lafiya

Published

on

images (3)

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Ƙaramin ministan lafiya da walwalar jama’a, Dr Iziaq Salako, ya nuna buƙatar dawo da taken nan na “Kasancewa bakar fata abin alfahari ne” wanda ke nuna kyawun kasancewa baƙi kuma ɗan Afirka domin kaucewa wa tunanin alaƙanta kyau da farar fata.

Salako ya bayyana hakan ne a yayin wani taron wayar da aka yi a ƙasar Gabon kan amfani da kayan shafe-shafe na bilicin (masu sa fata ta yi haske).

‎An Gurfanar Da Masoyan Da Suka Kai Wa Malamin Polytechnic Hari A Kano  

A cikin wani jawabi da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya samu a ranar Alhamis, a cikin jawabin, ministan ya yi kira ga fitattun mutane da suka yi shura – masu mabiya da yawa – da shugabannin da su riƙa kira ga mutane kan su rungumi halittarsu ta asali tare da yin watsi da sauya launin fatarsu don zama kyakkyawa.

“Ta hanyar haɗin guiwa, za mu iya magance matsalar yin bilicin da sa mutane su fahimci cewa akwai wasu hanyoyi da za su bi wajen fito da kyawunsu”

Ya ce ita ce kan gaba a duniya da kaso 77% na mata da ke amfani da kayan shafe-shafe na bilicin a duniya kamar yadda rahoton hukumar lafiya ta duniya ya nuna kamr yanda Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito

Advertisement

Ya ce wasu binciken ma sun nuna yadda ake samun mutane da yawa da ke sauya kaunin fatar jikinsu don su yi fari a Najeriya.

Sannan ya ce akwai sakamakon bincike na hukumar kare lafiyar masu amfani da kayan shafe-shafe (CSMP) wanda ya nuna cewa kaso 52% na kamfanonin da ke samar da kayan shafe-shafe na sanya sinadaran sa fata haske.

Salako ya ce akwai mutane da suka yi wa kalmar “toning” (gyara fata) mummunar fahimta da cewa daidai take da “bleaching” (sa fata ta yi haske) inda suke ɗaukar kamar bilicin ba shi da wata matsala.

Sai dai ya jaddada buƙatar fito da illar da amfani da kayan shafe-shafen bilicin ke da shi ga lafiya saboda suna ɗauke da sinadarai masu illa da a Turance ake kiransu da “mercury, hydroquinone, steroids, da heavy metals”

“waɗannan sinadarai suna lalata fata, da shafar wasu sassan jiki da jijiyoyi da haifar da cutar kansa.”

“Ƙaruwar yadda ake amfani da kayan shafe-shafe masu sa haske a Afirka, musamman a Najeriya, abin damuwa ne, don haka, akwai buƙatar wayar da kan al’umma da sa tsauraren dokoki da sauransu, domin yaƙi da wannan ɗabi’a.”

Advertisement

Daga nan ne Salako ya yaba wa ma’aikatar lafiya da hukumar NAFDAC kan irin matakan da suke ɗauka.

Ya kuma ce yakamata a yi amfani dokar kula da kayan shafe-shafe ta shekarar 2019 wadda ta haramta amfani da mayukan da suke sa fatar jiki haske kamar Mercury da ƙayyade yawan sinadarin ‘hydroquinone’ zuwa kaso 2% da za ayi amfani da shi.

“Sannan gwamnati na ƙoƙarin samar da dokoki na tantance kayan shafe-shafe domin cike giɓin da ke akwai wajen tabbatar da sun cika ƙa’idar da ake amfani da ita a duniya.”

Kamfanin dillancin labaran ya rawaito cewa nahiyar Africa na cigaba da zama kan gaba wajen amfani da kayan shafe-shafen yin bilicin.

A cewar wani rahoto na hukumkar lafiya ta duniya, yadda mata suke amfani da mayukan bilicin a nahiyar Afirka ya bambanta daga wannan ƙasa zuwa waccan.

Rahotan ya buga misali da yadda matan wasu ƙasashen Afirka ke amfani da mayukan bilicin kamar haka, Mali (25%), Afirka ta Kudu (kaso 32%), Ghana (kaso 39%) Senegal (kaso 50%), Congo-Brazzaville (66%).

Advertisement

Sai dai rahotan hukumar lafiya ta duniya, ya bayyana cewa kaso 77% na matan Najeriya suna amfani da mayukan masu sa fata ta yi haske kuma ta ɗaya a duniya.

Wannan ɗabi’a dai na da alaƙa da yadda sauran al’umma ke ɗaukar masu farar fata a matsayin kyawawa, masu kuɗi ko kuma waɗanda suka yi nasara.

Ƙasashen Afirka kamar Ghana da Afirka ta Kudu da Mali sun daɗe da haramta duk wani abin shafawa mai sa hasken fata, sai dai rashin aiwatar da dokar na cigaba da ba wa kayan shafe-shafe damar shiga kasuwanninsu har masu yi su saya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending