News
An Gurfanar Da Masoyan Da Suka Kai Wa Malamin Polytechnic Hari A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata ɗaliba daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, mai suna Khadija Hassan Chiranchi, da kuma saurayinta Khalid Hussain wanda aka fi sani da Baffa, sun gurfana a gaban kotun Shari’ar Musulunci kan zargin kai wa malami hari.
Rahotanni sun bayyana cewa, Khadija ta gayyato saurayinta Khalid zuwa ofishin malamin, Aliyu Hamza Abdullahi, wanda ta ce yana zame mata matsala a karatunta.
Kungiyar SERAP Ta Maka Shugaba Tinubu Da Hukumar Ncc A Kotu Kan Karan Kudin Kiran Waya Da Data
Dukkaninsu sun gurfana a kotu kan tuhume-tuhumen da suka haɗa da, haɗa baki, aikata daba, kutse da cin zarafi.
Sun musanta zargin da ake musu, inda suka ce kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.
Duk da haka, alƙalin kotun ya bayar da umarnin a tsare su a gidan yari har zuwa ranar 27 ga Fabrairu, 2025, don sake gurfanar da su.
Sai dai kuma, an zargi saurayin da mallakar makami mai hatsari, wanda ya amince da laifin.
Wanda a nan ne kotun ta ce tana da hurumin sauraron wannan ɓangaren na zargin, wanda ya sa aka ɗage shari’ar zuwa wannan rana domin ci gaba da sauraron ta.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
