News
Zan Jagoranci yiwa Madakin Gini Kiranye Daga Majalisar Tarayya, Domin Al’ummar Dala Basa Bukatar Wailcinsa —Waiya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamishinan yada labarai da alamurann cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya yace zai jagoranci yiwa Hon. Ali Sani Madakin Gini kiranye daga Majalisar Tarayya, kasancewar Alummar karamar Hukumar Dala da Kano basa bukatar wakilcinsa
Kwamared Waiya na wannan Batu ne yayin Taron masu ruwa da tsaki na karamar Hukumar Dala da Yan jamiyyar NNPP, Wanda aka gudanar a yau a dakin taro na Mumbayya dake nan Kano.
Kaso 77% Na Mata Da Ke Amfani Da Kayan Shafe-shafe Na Bilicin A Duniya Yan Najeriya —Ministan Lafiya
Daga nan Waiya yace karamar Hukumar Dala tana bukatar jagora jajirtacce Wanda zai Kai matsalolin Alummar yakin Majalisar wakilai Domin a magance su.
Kwamishinan ya kuma godewa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa tarin mukaman da ya baiwa Alummar karamar Hukumar Dala.
Taron ya samu halartar Shugabanni Jamiyyar NNPP a karamar Hukumar da masu Ruwa da tsaki, sannan dukkkan Yan Amanar Kwankwasiyya.
