Connect with us

News

AZUMI: Gara A Taimaka A Rage Farashin Abinci Fiye Da Ware Biliyoyi Don Rabo —Yasir Sani 

Published

on

images

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A duk shekara, musamman a lokacin azumi, gwamnati da wasu kungiyoyi kan ware biliyoyin kuɗi domin rabon abinci ga mabukata. Wannan mataki yana da amfani ga wasu, amma idan aka duba yadda hauhawar farashin kayan abinci ke shafar kowa, akwai bukatar yin duba da tsari mafi inganci.

Maimakon ware wadannan biliyoyi don rabon abinci ga wasu, zai fi dacewa a yi kokarin rage farashin kayan abinci gaba ɗaya, domin kowa ya iya siya ba tare da wahala ba. Hakan zai taimaka ga talaka fiye da bayar da abinci ga wasu kaɗan yayin da sauran jama’a ke fama da tsadar rayuwa.

Ƙudirin Sabunta Dokar Harajin VAT Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Zauren Majalisa

Masana tattalin arziki na ganin cewa, idan gwamnati ta shiga tsakani don daidaita farashin kayan abinci ta hanyar rage haraji, tallafawa manoma, ko hana hauhawar farashi maras tushe, hakan zai fi tasiri a kan rayuwar al’umma.

A ƙarshe, saukaka rayuwa ga kowa da rage farashin kayan abinci yana da fa’ida fiye da tsarin raba abinci ga mutane kaɗan. Wannan zai taimaka wajen samar da daidaito da wadatar abinci ga dukkan al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending