News
Ana Fargabar Masu Kwacen Babur Sun Hallaka Wani Mutum A Unguwar Kwachiri A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotanni daga jihar Kano sun tabbatar da cewa wani mutum da ke sana’ar achaba ya rasa ransa sakamakon harin da wasu da ake zargin barayin babur ne suka kai masa a daren Laraba.
Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a bakin titin da ke tsakanin Airport da unguwar Kwachiri, inda ɓata garin suka farmaki mutumin, suka yi masa rauni mai tsanani ta hanyar yanka shi, sannan suka tsere da babur ɗinsa.
AZUMI: Gara A Taimaka A Rage Farashin Abinci Fiye Da Ware Biliyoyi Don Rabo —Yasir Sani
Wannan lamari ya haifar da fargaba a tsakanin masu sana’ar achaba da ma al’ummar yankin, inda ake kira ga hukumomi da su dauki matakin da ya dace domin tabbatar da tsaro a wannan wuri da kuma dakile ayyukan masu aikata irin wannan danyen aiki.
Hukumomi dai ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba a yanzu, amma ana sa ran za a gudanar da bincike domin gano gaskiyar al’amarin da kuma daukar matakin da ya dace.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
