Connect with us

News

Mai Baiwa Gwamnan Kano Shawara Kan Hulda da Al’umma Ya Rasu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Mai Baiwa Gwamnan Kano Shawara Kan Hulda da Al’umma, Abdussalam Abiola Abdullateef Ya Rasu

Advertisement

Mai baiwa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, shawara na musamman kan hulda da al’umma, Alhaji Abdussalam Abiola Abdullateef ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Jami’an Hukumar Hisba Sun Kama Matasan Da Basu Yin Azumi Da Masu Askin Banza A Kano

Majiyoyi daga iyalinsa sun tabbatar da cewa Abdussalam ya rasu ne a ranar Asabar kuma an yi jana’izarsa da yammacin ranar a makabartar Hajji Camp da ke Kano.

Advertisement

Marigayin, wanda dan asalin jihar Osun ne, ya kammala karatunsa na digiri a fannin lissafi daga Jami’ar Bayero da ke Kano, kuma kwanan nan ya yi ritaya daga aikin Asibitin Koyarwa na National Orthopedic Hospital Dala, Kano.

A baya, ya rike mukamin mai baiwa tsohon gwamnan Kano, Engr. Rabiu Musa Kwankwaso shawara daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Advertisement

Allah ya jikansa da rahama, ya baiwa iyalai da masoya hakurin jure wannan rashi.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending