News
Al’ummar Darerawa Sunyi Kira Ga Gwamnatin Kano Don Magance Barazanar Zaizayar Kasa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Al’ummar Unguwar Darerawa ‘A’ dake mazabar ‘Yan Mata Gabas a karamar hukumar Fagge sun roki Gwamnatin Jihar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai musu dauki kan barazanar zaizayar kasa da ambaliyar ruwa da ke addabar yankin a duk lokacin damina.
Da yake gabatar da koken al’ummar yankin, Alhaji Abubakar Auwalu ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne sakamakon ginin magudanar ruwa da aka kasa kammalawa zuwa karshen titin, wanda hakan ke haddasa kwararar ruwa zuwa cikin gidajen jama’a a lokacin ruwan sama.
Alhaji Abubakar ya ce gidaje da dama sun rushe a daminar bara sakamakon ambaliya, inda ya kara da cewa tun shekaru goma da suka gabata, jama’ar yankin ke cikin fargabar barci a dararen da ake ruwan sama saboda tsoron iftila’in ambaliya da zaizayar kasa.
Shi ma a nasa bangaren, wani mai kishin cigaban al’umma, Malam Sharif Ahmad Sharif, ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar karamar hukumar Fagge da takwaransa na majalisar dokokin jihar da su kawo daukin gaggawa ta hanyar karasa aikin magudanar ruwa kafin damina ta kama.
Sharif Ahmad Sharif ya kuma bukaci gwamnati da ta saka yankin Darerawa ‘A’ da Kwaciri cikin aiyukan gwamnatin jihar na magance zaizayar kasa da ambaliyar ruwa don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
RADIO KANO
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
