Connect with us

News

Wuta Ta Kone Sabon Ginin Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Mata A Jami’ar Sokoto

Published

on

images 4 4 715x375
Spread the love

A ranar Talata da ta gabata, wata gobara ta kama sabon ginin ɗakunan kwanan ɗalibai mata na Jami’ar Jihar Sokoto, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin al’ummar jami’ar.

Gobarar, wadda ta tashi da misalin ƙarfe 3:30 na rana, ta ƙone gaba ɗaya sabon ginin da aka gina domin rage matsalar ƙarancin masaukai ga ɗalibai.

Waɗanda Zakkar Fidda-Kai Ta Wajaba A Kansu Da Muhimmancinta Ga Al’umma

Har yanzu dai ba a gano ainihin musabbabin tashin gobarar ba. Wata ɗaliba da ta tofa albarkacin bakinta kan lamarin ta ce, “Har yanzun, ba mu san abin da ya haifar da gobarar ba.”

Sai dai a lokacin da gobarar ta tashi, babu wata ɗaliba da ke cikin ginin, kasancewar an riga an sauya musu masauki bisa umarnin jami’ar.

Advertisement

Hukumomi dai har yanzu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba.

 

 

LEADSHIP

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *