News
Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Tsaftar Muhalli Na Watan Maris Saboda Shirye-shiryen Bikin Sallah
Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na watan Maris domin bai wa mazauna damar mayar da hankali kan shirye-shiryen bikin Sallah.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahiru Hashim, ya bayyana hakan, inda ya ce wannan mataki zai bai wa jama’a damar gudanar da bukukuwan karshen azumin Ramadan cikin kwanciyar hankali, tare da maraba da baƙin da ke shigowa cikin jihar.
Wuta Ta Kone Sabon Ginin Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Mata A Jami’ar Sokoto
Sai dai, duk da dakatarwar, za a ci gaba da gudanar da tsafta a ofisoshin gwamnati, tashoshin mota, da kasuwanni a ranar 28 ga Maris, 2025. Ma’aikatar ta jaddada kudirinta na kiyaye tsaftar muhalli, tare da mutunta al’adu da addini.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
