Connect with us

News

Girgizar Ƙasa Ta Kashe Mutane 144, Ta Jikkata 732 a Myanmar

Published

on

Myanmar earthquake death 696x348 1

Aƙalla mutane 144 ne suka rasa rayukansu tare da wasu 732 da suka samu raunuka sakamakon wata girgizar ƙasa da ta afku a yankin Myanmar, kusa da ƙasar Thailand, a ranar Juma’a, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.

Girgizar ƙasar ta haddasa rushewar gidaje da gine-ginen da suka mamaye ɗaruruwan mil. Hukumomi sun bayyana cewa ana cigaba da tantance girman hasarar da aka tafka, yayin da ake ci gaba da gano gawawwaki da kuma ceto waɗanda suka makale a cikin baraguzan gine-gine.

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Matar Da Ta Sace Tare Da Kashe Yarinya ‘Yar Shekara 8 A Kano

Tun bayan faruwar lamarin, gwamnatin Myanmar ta ayyana dokar ta-ɓaci a babban birninta da kuma birni na biyu mafi girma a ƙasar, domin bai wa hukumomin ceto damar gudanar da aikinsu cikin gaggawa. Haka kuma, birnin Bangkok na ƙasar Thailand ya ɗauki matakan gaggawa don fuskantar tasirin girgizar.

Ana fargabar cewa adadin waɗanda suka rasa rayukansu na iya ƙaruwa, duba da yadda ake cigaba da gano karin gawawwaki a wuraren da girgizar ƙasar tafi shafa.

 

BLUEPRINT

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending