News
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Matar Da Ta Sace Tare Da Kashe Yarinya ‘Yar Shekara 8 A Kano
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wata matar aure, Fadila Adamu, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun ta da laifin sace wata yarinya ‘yar shekara takwas tare da jefata a rijiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Mai shari’a Yusuf Muhammad-Ubale ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, yana mai cewa masu gabatar da kara sun gabatar da hujjoji masu karfi fiye da shakku, wanda ya tabbatar da laifin matar.
Dole A Hukunta Masu Hannu A Kisan ‘Yan Arewa A Edo – Kungiyar Who Is Fixing The North?
“Ina yanke wa wacce ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda sace yarinyar da jefata cikin rijiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta,” in ji Mai shari’a Muhammad-Ubale.
Lauyan masu gabatar da kara, Lamido Abba-Sorondinki, ya bayyana wa kotu cewa lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Yuli, 2019, a unguwar Tudun Wada, Kano.
Bincike ya nuna cewa matar ta sace yarinyar ne da misalin karfe 4:45 na yamma, sannan ta kaita gidanta da ke unguwar Sabuwar Gandu, inda ta shaida wa ‘yar uwarta cewa yarinyar ‘yar wata kawarta ce da ta tafi Ghana.
Hukuncin ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin ya zama darasi ga masu aikata laifukan irin wannan.
DAILY NIGERIAN
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
