News
Dole A Hukunta Masu Hannu A Kisan ‘Yan Arewa A Edo – Kungiyar Who Is Fixing The North?
Shugaban Kungiyar Who Is Fixing The North?, Mustapha Dawood (Sir Sa’e), ya yi kakkausar suka kan kisan gilla da aka yi wa wasu ‘yan Arewa 16 da ke kan hanyarsu ta dawowa Kano daga Jihar Edo.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, shugaban kungiyar ya bayyana wannan harin a matsayin abin takaici da ke kara nuna yadda daukar doka a hannu ke barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasa.
Da Dumi-Dumi : Yan Sandan Kano Sun Ce Babu Hawan Sallah A Bana
Kungiyar ta jaddada cewa kowanne dan kasa na da ‘yancin yin tafiye-tafiye cikin ‘yanci ba tare da wani cin zarafi ko fuskantar barazana ba. Saboda haka, ta bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike mai zurfi tare da hukunta duk wadanda aka samu da hannu a wannan mummunan kisa.
Bugu da kari, kungiyar ta aikewa da sakon ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kano, ‘yan uwa da iyalan mamatan, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu, ya ba su rahama, kuma ya bai wa iyalansu hakurin jure wannan rashi mai girma.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
