Connect with us

News

DMCSA Tare Da Gidauniyar Gates Da C4SD Sun Horas Da Jami’an Lafiya Kan Sarrafa Kayan Tazarar Iyali A Kano ‎

Published

on

IMG 20250418 WA0016
Babban Daraktan DMCSA, Pharm. Gali Sule
Spread the love

A kokarin inganta lafiyar al’umma da dorewar ci gaban jama’a, Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti ta Jihar Kano (DMCSA), tare da hadin gwiwar kungiyar Capacity for Sustainable Development (C4SD) da tallafin Gidauniyar Bill and Melinda Gates, sun shirya taron horaswa na kwanaki biyu ga shugabannin kula da lafiyar mata masu juna biyu (MCH) da jami’an kula da magunguna.

‎An gudanar da wannan horo ne domin kara basira da kwarewar mahalarta a fannin sarrafa kayan tazarar iyali da kuma tabbatar da isar da su cikin inganci ga mabukata a yankunan karkara da birane.

Dole Al’umma Su Tashi Tsaye Su Kare Kansu — Gwamna Mutfwang

‎Da yake bude taron, sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Pharm. Aminu Bashir, wanda ya wakilci kwamishinan lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya jaddada muhimmancin hada kayan tazarar iyali da sauran kayayyakin lafiya a tsarin kiwon lafiya.

Advertisement

‎A cewarsa, “Sarrafa kayan tazarar iyali yadda ya kamata da kuma isar da su har zuwa matakin karshe, na da matukar mahimmanci wajen tabbatar da lafiyar mata da yara, tare da rage kashe kudi da lokaci, da kuma bin doka da oda.”

‎Pharm. Bashir ya kara da cewa horon zai taimaka wajen kara kwarewa ga jami’an da ke da alhakin rarraba wadannan kayayyaki a matakin farko na kiwon lafiya.

‎A nasa jawabin maraba, Babban Daraktan DMCSA, Pharm. Gali Sule, ya bayyana cewa wannan shiri na cikin sabon tsarin kasa na hada kayan lafiya da magunguna domin isar da su kyauta zuwa cibiyoyin lafiya. Ya kuma jaddada kudirin hukumar na ci gaba da hadin gwiwa da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, domin fadada shirin zuwa sassan jihar baki daya.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *