News
Dole Al’umma Su Tashi Tsaye Su Kare Kansu — Gwamna Mutfwang
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa lokaci ya yi da al’umma za su tashi tsaye domin kare kansu daga hare-haren da suka zama ruwan dare a yankunan jihar, musamman a ƙaramar hukumar Bassa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai yankin Kwall a masarautar Iregwe, inda aka kai hari na baya-bayan nan da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 50 a garuruwan Zike da Kimakpa.
A cewar rahoton PREMIUM TIMES, fiye da mutane 100 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da ake zargin wasu makiyaya ne ke kaiwa a cikin makonni biyu da suka gabata.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa hare-haren da ake kaiwa a jihar sun janyo tsaiko mai tsanani ga ci gaban jihar, yana mai cewa: “Rashin tsaro da ta’addanci suna hana jihar Filato cimma burinta na ci gaba mai ɗorewa.”
Ya kara da cewa tun daga fara mulkinsa a shekarar 2023, gwamnatin sa ta zuba jari mai yawa a fannin tsaro, musamman ta hanyar amfani da fasaha domin dakile hare-haren.
“Mun ɗauki matakan gaggawa tare da zuba kuɗi mai yawa wajen samar da kayan aikin zamani domin tinkarar matsalar tsaro,” in ji shi.
Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda matsalolin tsaro suka hana manoma fita gona, wanda hakan ke shafar rayuwar tattalin arziki da walwalar al’ummar yankin.
Kiraye-kirayen Kariya daga Al’umma
Gwamna Mutfwang ya jaddada cewa babu wata nasara a fannin tsaro da za a iya samu sai al’umma sun ɗauki matakin kare kansu.
“Mun kai wani mataki da dole ne kowacce al’umma ta tashi tsaye domin kare kanta,” in ji gwamnan.
Sai dai ya bayyana cewa wannan kira ba yana nufin ɗaukar doka a hannu ba ne, inda ya ce dole ne a tabbatar da sahihancin kowace ƙungiyar tsaro da ke aiki a yankuna.
Gwamnan ya gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan goyon bayan da yake baiwa jihar, tare da kiran jami’an tsaro da su ƙara himma domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka dabaibaye yankin.
“Mun zo nan ne domin tabbatar muku cewa gwamnati tare da jami’an tsaro za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa don kare rayukan al’umma”.
Ya ce Jihar Filato ba ita kaɗai ba ce ke fuskantar irin wannan matsalar. Jihohin Neja, Benuwai, Taraba da Kaduna na daga cikin wuraren da hare-haren ‘yan bindiga da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya ke faruwa akai-akai.
Akwai masu sukar irin wannan kira da Mutfwang ya yi, suna cewa hakan na iya ƙara haddasa rikice-rikice, ganin cewa yawaitar makamai a hannun jama’a na iya kara tayar da ƙura a cikin al’umma.
A cewar wasu masana tsaro, dole ne a inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma tare da tabbatar da cewa. kowane mataki yana cikin bin doka da oda.
