News
SATAR AMSA: WAEC Ta Dakatar Lasisin Makarantu 574
Hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire ta Yammacin Afrika (WAEC) reshen Najeriya, ta bayyana kwace lasisin makarantu 574 da aka samu da laifin aikata maguɗi a jarrabawar da ta gabata.
Shugaban ofishin WAEC na Najeriya, Dr. Amos Dangut, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Legas a ranar Alhamis.
Fursunoni 62 Sun Kammala Karatun Sakandare A Gidan Gyaran Hali Na Kano
Dangut ya ce an riga an tura jerin sunayen makarantu da aka soke lasisin su zuwa ga gwamnatin tarayya, domin daukar mataki na gaba.
Ya bayyana cewa daga yanzu, ba za a gudanar da jarrabawa a cikin wadannan makarantu ba, har sai an tabbatar da cikakken gyara da bin doka. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jarrabawar WAEC ta shekarar 2025 (WASSCE) ke gab da farawa a ranar Alhamis, 24 ga Afrilu, 2025.
Dangut ya bayyana cewa yawan daliban da suka yi rijista domin jarrabawar WASSCE ta bana ya kai 1,973,253 daga makarantu 23,554, inda 979,228 daga cikinsu maza ne, yayin da mata suka fi yawa da 994,025.
Ya kara da cewa hukumar ta WAEC tana amfani da sabbin fasahohi domin inganta tsarin gudanar da jarrabawar. Ciki har da fara jarrabawar kwamfuta ta farko wato CB-WASSCE, wanda ke nuna alamar sauyi da ci gaba a tsarin tantance cancanta da nagarta a bangaren ilimi.
WAEC ta jaddada cewa wannan mataki na dakatar da makarantu masu hannu a maguɗi na daga cikin shirin ta na tabbatar da gaskiya, adalci da kuma kare amincin jarrabawar a Najeriya da ma sauran kasashen da ke karkashin kulawarta.
