News
An Tura Ƙarin Dakarun Soji 850 Domin Tabbatar Da Tsaro A Filato
Shugaban rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Janar Waidi Shuaibu ya bada umarnin tura ƙarin sojoji 850 Jihar Filato domin tabbatar da tsaro sakamakon tashin hankalin da ya yi sanadiyar asarar rayuka a jihar.
Mai magana da yawun rundunar sojin dake aikin samar da zaman lafiya a jihar, Kaftin Chinonso Polycarp Oteh ne ya sanar da matakin, a dai dai lokacin da hukumomi ke lalubo hanyar dawo da zaman lafiya a garin Jos, bayan ƙazamin harin da ya laƙume rayukan mutane a ranar lahadin da ta gabata.
Tsohon Gwamnan Kano, Abubakar Rimi, Ya Cika Shekaru 16 Da Rasuwa
Oteh ya ce ana saran tura ƙarin sojojin ya taimaka wa waɗanda ke aiki a jihar wajen kare lafiya da kuma dukiyoyin jama’a a fadin jihar baki ɗaya.
Janar Shuaibu da ya ziyarci jihar domin ganewa kan sa halin da ake ciki, ya buƙaci sojojin da su tabbatar da gudanar da aikin su kamar yadda doka ta tanada da kuma mutunta kare rayukan jama’a.
Shugaban ya tabbatar wa dakarun cewar an tanadar musu da isassun kayan aiki da kuma haƙƙoƙin su domin ganin sun samu nasarar da ta kamata.
Kakakin rundunar sojin ya ce an ɗebo sojojin 850 daga Abuja da Kaduna domin taimakawa na Filato gudanar da aikin samar da tsaron.
A ziyarar da ya kai jihar ta Filato jiya, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin cewar ba za’a sake ganin irin tashin hankalin da aka gani a garin Jos ba.
A jawabin da ya yiwa masu ruwa da tsaki da a jihar, shugaban ya ce fatar sa ita ce na ganin garin Jos ya koma matsayin sa na da wanda suka sani, na zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali.
