Connect with us

News

Majalisa Wakilai Ta Buƙaci A Samar Cibiyar Rubuta JAMB A Kowace Ƙaramar Hukuma

Published

on

jamb exam1 (1)

 

Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci a samar da cibiyar rubuta Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta UTME guda ɗaya aƙalla a kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin ƙasar.

Advertisement

Ƴanmajalisar sun bayyana hakan ne a zaman majalisa da suka gudanar a ranar Alhamis, bayan da Hukumar JAMB ta amsa samun matsalolin da suka shafi gudanar da jarrabawar bana ta 2025.

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane Sama da 200 A Zamfara – Inji Ɗan Majalisa

A cewar ‘yan majalisar, samar da waɗannan cibiyoyin zai taimaka wajen hana maimaituwar irin waɗannan matsalolin a nan gaba.

Advertisement

Majalisar ta kuma buƙaci ɗalibai da iyaye su kwantar da hankalinsu bayan amincewar JAMB cewa an samu kura-kurai a jarrabawar bana.

A bara, Majalisar Dattawa ta kawo irin wannan ƙudiri, inda ta ce za a ware kudi a kasafin shekarar 2026 domin samar da cibiyoyin rubuta jarabawar jamb (CBT) a dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar.

Advertisement

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan makarantun gaba da sakandire da TETFUND, Mohammed Dandutse, ya bayyana hakan yayin da yake sa ido kan yadda jarrabawar UTME ta 2025 ke gudana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending